Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Al-Burhan ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai jiya a kasar Masar, inda ya ce, ra'ayoyin Masar da Sudan dangane da dukkanin batutuwan da suka shafi yankin sun daya, kuma Masar din tana goyon bayan sauyin dimokradiyya a Sudan, kuma ba za ta daina yin hakan ba.
Shugaban kwamitin rikon kwarya na Sudan ya bayyana karara cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangaren soji a Sudan da sauran bangarorin siyasar kasar, wanda ke nuni da cewa ba mu da wani zabi illa tattaunawa.
Al-Burhan ya ce, "Muna fatan ganin an samu hadin kai mai karfi da Masar," in ji Al-Burhan, yana mai jaddada cewa, ana daukar hakikanin matakai a wannan fanni.
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi ya karbi bakuncin Laftanar Janar na farko Abdel Fattah Al-Burhan a fadar gwamnatin masar, inda aka gudanar da bikin liyafar tarbarsa a hukumance.
342/